Back to Top
Tarihin Manzon Allah (S.A.W) Screenshot 0
Tarihin Manzon Allah (S.A.W) Screenshot 1
Tarihin Manzon Allah (S.A.W) Screenshot 2
Tarihin Manzon Allah (S.A.W) Screenshot 3
Free website generator for mobile apps; privacy policy, app-ads.txt support and more... AppPage.net

About Tarihin Manzon Allah (S.A.W)

Wannan application yana dauke da tarihi na Annabi Mohammead (S.W.A), wanda wani shahararen marubucin tarihi ya wallafashi da harshen larabci.Shine aka fassara shi izowa harshen hausa domin amfanarwa ga al'umar Hausawa wadan da ke neman ililmi akan cikeken tarihin Manzo Allah (S.W.A).
Littafin ya kunshi gundrin rayuwar Manzon Allah tunda ga kan haihuwar sa, da kuma irin gwagwarmayar da yasha kafin a fara saukar masa da wahayi. Littafin bai tsaya nan ba kadai,ya kara bamu asali da kuma tarihi na mussulunci tunda daga kan annabi na farko, wato annabi Adam (AS) zuwa sauran annabawa a takaice.shi dai wannan littafi yafi bada karfi akan kafuwar musulunci da kuma rayuwar Annabi Mohammad (S.A.W).
ina fatan wannan application wanda akayi shi don sauwakin amfani zai zamo abin amfanarwa ga al'umar musulmi.
Don Allah idan har kajin dadin amfani da wannan application kayi kokari ka yadashi don wasu suma su amfana.

Takaiccen tarihin manzon Allah.

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan ʿAbdullahi (Sallallahu ʿalaihi wa sallam).

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in.

Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi.

Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma waxanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a voye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

Yaqoqinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yaqar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi xauki ba daxi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.

Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi xan Akhdabl.

'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Faxima (a.s) a wani qaulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMuxallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Xalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-muqawwam da Abu Lahab da Abbas.

Similar Apps

KITABUT TAUHID

KITABUT TAUHID

4.7

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai.Dukkan godiya ta tabbata...

Sheikh Albani Zaria Tafseer

Sheikh Albani Zaria Tafseer

5.0

Wannan application na dauke da tafseer naa alqurani mai girma wanda Sheikh...

Sheikh Albani Zaria Lectures m

Sheikh Albani Zaria Lectures m

5.0

Wannan application na dauke da wasu zababu daga lectures da Sheikh Muhammad...

Muwadda Malik Dr Ahmad BUK

Muwadda Malik Dr Ahmad BUK

4.0

Wannan application na dauke da karatun Muwadda Malik na babban malamin sunna...

Kundin Tarihi Sheikh Aminu Dau

Kundin Tarihi Sheikh Aminu Dau

0.0

Wannan application yana dauke da tarihe-tarihe na musulunci tunga kan annabawa Allah...

Sheikh Jafar Umdatul Ahkam mp3

Sheikh Jafar Umdatul Ahkam mp3

0.0

Wannan application na dauke da karatun baban littafin hunnce-hukuce wato umtadul ahkam,...

Frequently Asked Questions(FAQ)

Wannan application yana dauke da sunaye domin wani marubucin tarihi?

Shine, wannan application yana dauke da tarihin Manzon Allah (S.W.A).

Dokokin tarihin mai dauke da harshen sarfu a wannan application?

Harshen sarfuka a wannan application shine harshen Hausa.
author
Allah ya bamu Albarkacin Annabi Muhammad (S .A.W).
SARATU SAE
author
Saw allah biya
Sani Mohammed
author
Aslm Alkm, Malam has done justice to his presentation , but since Malam is not MAHSOOM, He is subject be guided corrected and be correcred. Masha-Allah. Jazakallahu Khair. Mslm.
Haruna Muhammad Hassana
author
I love prophet muhammad S.A.W sooooo much thank u for dis app
Zainab Ahmed
author
Thanks for those who created this Application 👌 I can Rate it 100 Stars Because I love Prophet Muhammad S,A,W 💯😍😍
YUSUF SANI
author
Superb
ARC ABDULLAHI SAIDU