Back to Top
KITABUT TAUHID Screenshot 0
KITABUT TAUHID Screenshot 1
KITABUT TAUHID Screenshot 2
KITABUT TAUHID Screenshot 3
Free website generator for mobile apps; privacy policy, app-ads.txt support and more... AppPage.net

About KITABUT TAUHID

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai.
Dukkan godiya ta tabbata a gareshi, kuma tsira da
amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da
iyalanshi da kuma sahabbanshi baki-daya.
Bayan haka, wannan fassarar littafin “Kitabut Tauhid.
ne, wanda Shehun malami Dr. Saleh bin Fauzan bin
Abdallah Alfauzan ya wallafa, wannan malami fitaccan
malami ne mamba ne a majalisar manyan malamai ta
kasar Saudi Arebiya, kuma mamba a kwamitin dindindin
na fatawa da kuma bincike akan ilimi.
Wannan littafi na Tauhidi da wannan malami ya wallafa
ya taba bangarori da dama wadanda ake matukar neman
bayanan su a daidai wannan lokaci, zaka iya cewa littafin
ya zo ne a daidai lokacin da ake matukar bukatarsa.
Mawallafin littafin ya fara kawo mukiddima ne sannan
ya biyo shi da babi-babi har guda hudu, sannan akar
kashin kowanne babi akwai fasali-fasali da malam ya
kawo. Babi na farko yana kunshe ne da fasali biyar, a
yayinda babi na biyu kuma yake kunshe da fasali-fasali
har goma sha-daya, shi kuwa babi na uku yana dauke ne
da fasali-fasali har guda shida, ayayin da babi na karshe
wato babi na hudu yake dauke da fasalai har guda hudu.
Wannan littafi kamar yadda sunansa yake ‘Kitabut
Tauhid’, kuma haka na Shehun malamin nan wato
Sheikh Muhammad dan Abdulwahhab yake da ‘Kitabut
Tauhid’ to amma sun yi tarayyane a suna amma sun sha
banban a irin bayanan da suke dauke da shi, duk da
bayanaine na tauhidi da kowanne yake da shi, saidai
bangarorin da kowa ya dauka ya yi bayani daban-daban
ne, saboda haka ana bukatar ka hada su duka ka mallake
su, Allah ya anfanar da mu da su baki-daya.
Lalle akwaimatukar bukatar a karantar da wannan littafi
a makarantu da masallatai da kuma wuraran fadakarwa a
kuma yada shi, saboda matukar muhimmancin da yake da
shi da kuma yadda ya tabo wadansu bayanai da ake
aikatawa a wannan lokacin da suke bukatar irin
wadannan malamai su yi bayaninsu.
Allah ya sakawa wannan malami da kuma wadanda suka yada wannan littafi Allah ya saka musu da alheri.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.

za kuma a iya samun wasu karatuttukan na wasu malam irin su sheikh jafar mahmud adam, sheikh albani zariya,sheikh ali isah fantami, shiekh kabir gombe.

Akwai karatun alqur'ani na wasu manyan makaranta kamar
complete quran offline by sheikh abdulrahman al-sudais mp3
beautiful quran recitation by sheikh maher almuquiy mp3
complete quran offline by shiekh abdolbasit mpe
quran recitation by mishary alfasy mp3 offline and so on

Don Allah idan har kaji dadin amfani da wannan littafi to ka taimaka kayi sharing din sa ga sauran yan uwa musulmai domin su ma su samu su amfana.
kuma kada a manta ayi rating na wannan application .

Similar Apps

Hausa Fashion Styles

Hausa Fashion Styles

0.0

Wannnan application mai suna hausa fashion styles na dauke da kala-kala na...

Nigerian Food Recipes

Nigerian Food Recipes

5.0

This application Nigerian food recipes contain almost all the Nigerian food recipes...

Tarihin Manzon Allah (S.A.W)

Tarihin Manzon Allah (S.A.W)

0.0

Wannan application yana dauke da tarihi na Annabi Mohammead (S.W.A), wanda wani...

Daily Dua & Azkar

Daily Dua & Azkar

4.9

Download this free daily dua & Azkar Islamic app to learn very...

Sheikh Albani Zaria Lectures m

Sheikh Albani Zaria Lectures m

5.0

Wannan application na dauke da wasu zababu daga lectures da Sheikh Muhammad...

Muwadda Malik Dr Ahmad BUK

Muwadda Malik Dr Ahmad BUK

4.1

Wannan application na dauke da karatun Muwadda Malik na babban malamin sunna...

Frequently Asked Questions(FAQ)

Wannan littafi mai yawan rahama mai yawan jinkai ne?

Na'am, wannan littafi ne mai yawan rahama mai yawan jinkai.
author
Good blessing you
Masahudu Gaiman
author
Jazakh Allah khai
Saidu Sani
author
Nice
mubarak abdulrazak
author
Excellent
zakari usman
author
Alhamdullilahi allah yasaka da alkhairi
Iliyasu Abdulrazak
author
Jazakallahu Kaira May Allah reward you with jannahtul firdaus
Abdullahi hassan