Back to Top
HANYOYIN WARAKA Screenshot 0
HANYOYIN WARAKA Screenshot 1
HANYOYIN WARAKA Screenshot 2
HANYOYIN WARAKA Screenshot 3
Free website generator for mobile apps; privacy policy, app-ads.txt support and more... AppPage.net

About HANYOYIN WARAKA

Wannan littafin/application Mai suna hanyoyin Waraka a Tafin Hannunka ta ƙunshi bayanai da suka shafi Sihiri da rabe-rabensa, maita,hassada da sauran cututtukan da al'umma ke fama da su da yadda za a magance waɗannan Cututtuka ta hanyar amfani da ayoyin Alkur'ani mai girma, addu'o'i da kuma magungunan gargajiya wanda aka daɗe ana amfani da su shekaru dubbai da suka gabata.

Na yi tunanin rubuta wannan littafin tare da haɗa wannan application ɗin ne bayan na yi dogon na nazari cewa lallai al'ummar mu musamman al'ummar Musulmi masu amfani da harshen Hausa suna da buƙatuwa su san menene Sihiri?, maita, hassada da illolin da suke yi wa jama'a da kuma hanyar warware su. Bugu da ƙari a duniyar Musulunci an yi rubuce-rubuce da dama akan waɗannan cututtuka da harsuna daban-daban musamman ma harshen larabci amma mu anan akwai ƙaranci littatafan da aka rubuta su da harshen Hausa wannan ya sanya na ɗauki abin rubutu da faɗa cikin bincike domin bada tawa guduwar abin da ya sauƙa.
Wannan littafin/application ta tattaro ayoyi Alkur'ani Mai girma da hadisai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam) da kuma bayanai na malamai da yadda za a samu waraka daga cututtuka daban-daban da kuma addu'o'in nema biyan buƙata da fita daga ƙunci. A cikin wannan binciken mun yi amfani da gogayyar da muke da ita na tsawon shekaru sama da ishirin (20yrs) muna bada maganin gargajiya (Islamic Medicine) hakan ya ba mu damar kawo hanyoyi da dama da muke amfani da su wa jama'a kuma suke samun waraka da iznin Allah Subhanahu Wata'ala. Dan haka wannan manhajar zata taimakawa jama'a sosai wajen magance Cututtukan da dama da kuma samun mafita daga matsalolinsu na yau da kullum.
Muna rokon Allah ya sanya aikin nan da muka yi ta zama karɓaɓɓe kuma ya kasance sadaƙatut-jariya garemu a bayan wafatin mu.

Similar Apps

الرقية الشرعية الشاملة

الرقية الشرعية الشاملة

0.0

This app is a compositions of Quranic verses which can use for...

Shebelinks Bundles

Shebelinks Bundles

0.0

We sell internet Data, Airtime, TV Cable subscription at affordable price.Our website...

SAUKAKEN FASSARAR AL-KUR'ANI.

SAUKAKEN FASSARAR AL-KUR'ANI.

0.0

SASSAUQAR TARJAMAR MA'ANAR AYOYIN ALQUR'ANI MAI GIRMA CIKIN HARSHEN HAUSAJIZI'IN NA 30...

Imi Bundle

Imi Bundle

0.0

Enjoy the best modern solution VTU service from imibundle.We offer instant recharge...

Koyon Sallah A Saukake

Koyon Sallah A Saukake

0.0

Wannan Manhajar mai suna koyon sallah a sauƙaƙe bisa koyarwar ahlulbaiti (a.s),...

Nurul Arsh

Nurul Arsh

0.0

Nurul- Arsh - Collection of supplications/Duas Narrated from the holy Prophet Muhammad...