Back to Top
Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Usul al-Iman Mp3 Screenshot 0
Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Usul al-Iman Mp3 Screenshot 1
Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Usul al-Iman Mp3 Screenshot 2
Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Usul al-Iman Mp3 Screenshot 3
Free website generator for mobile apps; privacy policy, app-ads.txt support and more... AppPage.net

About Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Usul al-Iman Mp3

Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa Barakatuh.

Wannan app yana dauke da Sharhin Usul al-Iman Mp3 na Sheikh Jafar Mahmoud Adam Mp3 Offline.

Allah ya sakawa Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya kuma jikansa.

Domin samun sauran apps na Sheikh Jafar da sauran manyan malamai na sunnah duba (rrnapps) free Hausa Islamic apps dake cikin play store

Don Allah a taimaka a yi sharing na Usulul Iman ta facebook, whatsapp, twitter da sauran social media domin sauran yan uwa musulmi su amfana.
Kada kuma a manta ayi rating na wannnan application five star.

*Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam

An haifi marigayi SheikhJa'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai
girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam
Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja,
wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma
Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Sharhin Usul al-Iman , Sharhin Kashf ush-Shubuhaat, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar
(Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.
Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.

Similar Apps

Medical X-Ray Interpretation w

Medical X-Ray Interpretation w

2.8

The chest radiograph is a very commonly requested examination and it is...

Vagina Vulva Care-Keep Healthy

Vagina Vulva Care-Keep Healthy

4.6

The content of this app Tips to Keep Your Vagina Happy +...

ECG / EKG Rhythm Step-by-Step

ECG / EKG Rhythm Step-by-Step

4.2

An ECG stands for an "electrocardiogram," which is a test that measures...

Mazan Jiya - Audio Mp3

Mazan Jiya - Audio Mp3

4.3

Wannan App ne Audio Mp3 yana dauke da Littafin nan mai suna...

Mazan Jiya Na Uku (3) - Audio

Mazan Jiya Na Uku (3) - Audio

4.0

Wannan App ne Audio Mp3 yana dauke da Littafin nan mai suna...

Advances in Ultrasound in Obst

Advances in Ultrasound in Obst

5.0

The International Society of Ultrasound in Obstetrics and Gynecology (ISUOG) recommends that...

author
Wonderful!
A Google user
author
The Sheikh Jafar (Rahimatullah) lectures are very educative and inspiring.
Abdullahi Yusuf Salisu
author
Masha allah
kedir mohammed
author
The app is very important to muslims life.
A Google user