Back to Top
Ko kun San? Screenshot 0
Ko kun San? Screenshot 1
Ko kun San? Screenshot 2
Ko kun San? Screenshot 3
Free website generator for mobile apps; privacy policy, app-ads.txt support and more... AppPage.net

About Ko kun San?

Ko kun san manhaja ce dana tsara ta domin kawo muku abubuwan daya kamata ace kun sani waɗan zai yi wuya ace kun same su a wani guri domin na tattaro bayanan dake cikin wannan manhajarce daka sassa daban daban.

Irin wannan manhajar zata kunshi bayanai masu tarin yawa don haka na tattaro abubuwan da nake ganin cewa zasu fi ɗaukan hankali ne kawai. Domin koda na sanya bayanai miliyan ɗaya ne banyi tsammanin na kammala ba. na tattaro bayanai da suka shafi tarihi, kimiyya da fasaha, psychology da sauran fannoni.


1. Ko kun san Annobar yunwa mafi muni da aka taɓa yi a tarihin duniya ita ce wacce aka yi a shekara ta 1932 zuwa 1933 a ƙasar Sin (China) inda mutane sama da miliyan arba'in suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan bala'in yunwar.
2. Ko kun san Yaƙi mafi muni da aka taɓa yi a tarihin Nigeria shine yaƙin basasar shekara ta 1967, wato yaƙin biafra, lokacin da iyamurai suka ayyana ɓallewa daga Nigeria. Kimanin mutane miliyan ɗaya suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan yaƙin.
3. Jihar Kano itace jiha mafi yawan jama'a a Nigeria.
4. Lalacewar ƙwaƙwalwa zai iya aukuwa ne kawai idan zafin zazzaɓi ya kai 107.6° farenheit.
5. An yi dashen zuciya na farko ne a 3 Dec 1967.
6. Tururuwa basa yin barci.
7. Baza ka iya kashe kanka ta hanyar riƙe nunfashinka ba.
8. Cakuleti zai iya kashe karnuka, domin ya ƙunshi sinadarin theobromine wanda yake shafan zuciyoyinsu da jijiyoyi.
9. Dodon koƙi zai iya yin barcin shekaru uku.
10. Zuma ce kawai abincin da baya lalacewa.
11. Idanun jarirai ba za su iya yin hawaye ba har sai sun kai makonni shida zuwa takwas a duniya.
12. Nigeria wacce take da yaruka 521, itace ta huɗu a yawan yaruka a duniya.
13. Turawan ƙasar Portugal sun iso Nigeria a shekara ta 1472.
14. A shekara ta 1880 Turawan Birtaniya suka fara mamaye kudancin Nigeria, amma sai a shekara ta 1903 suka fara mamaye arewacin Nigeria.

Domin sanin waɗannan bayanan dama wasu sauran ɗaruruwan bayanai sai ka saukar da wannan manhajar.

Similar Apps

English Hausa Kamus Dictionary

English Hausa Kamus Dictionary

4.7

This app is an offline English to Hausa comprehensive bilingual Dictionary (or...

Koyon Turanci

Koyon Turanci

0.0

Learning English lessons with Hausa descriptions where applicable for English learners and...

Mu koyi Turanci

Mu koyi Turanci

0.0

Darussan dake cikin wannan manhajar sune kamar haka:1. Text to speech2. Kalmomin...

Learn Hausa Grammar with Audio

Learn Hausa Grammar with Audio

0.0

Learn Hausa Grammar in English with audio pronunciation of Hausa sentence, phrases...

Love Psychology

Love Psychology

0.0

This app deals with love and marriage issues.The contents of this app...

Learn Hausa Alphabets

Learn Hausa Alphabets

0.0

Five lessons included, you can learn how to read and write Hausa...

author
Allah ya taimaka nice this app very much
Aliyu Boy Tv
author
I like this app wlh?
aliyu muhammad
author
Mlm app yayi gsky num ta whatsapp
DUNIYAR HAUSAWA TV
author
Naji dadin wannan app din sosai Ina fatan za'a karo mana wasu
Sani Master
author
Good work
Umar Muhammad
author
Yana da dadin ilimintuwa da taimakawa
Hacking ???