Back to Top
Al Quran Shine Mafi Kyau Zance Screenshot 0
Al Quran Shine Mafi Kyau Zance Screenshot 1
Al Quran Shine Mafi Kyau Zance Screenshot 2
Al Quran Shine Mafi Kyau Zance Screenshot 3
Free website generator for mobile apps; privacy policy, app-ads.txt support and more... AppPage.net

About Al Quran Shine Mafi Kyau Zance

Alqur’ani mai girma, maganar Allah ne, sannan kuma littafin sa ne mai girma, shi ba kamar sauran gamagarin maganganu bane, domin saukakke ne daga mai hikima abin godiya.
Don haka ne Allah madaukakin sarki ya shar’anta ma na wasu ladubba da ya wajaba mu lura da su wajen karatun Alqur’ani, domin girmama sha’anin sa, da daukaka matsayin sa.
Ya shar’antawa wanda zai karanta shi ya kasance mai tsarki, kuma ya kasance mai kankan da kai, tare da lura da tadabburin sa, da dai sauransu.
Yan uwa masu daraja, Hakika babu wata babbar ni’ima da Allah ya yiwa wannan al’ummah bayan ni’imar aiko da Annabi Muhammad (SAW) kamar ba mu Alqur’ani mai girma. Mu rike Alqur’ani domin riko da shi alkhairi ne duniya da lahira.
Domin ma’abocin karanta alqur’ani a kowanne lokaci zaka same shi cikin yalwar farin ciki, wofantar da shi kuma al’amari da ka iya jefa mutum a cikin rudanin rayuwa.
Allah ya saukar da Alqur’ani ta hanyar daya daga cikin Mala’iku, wato Mala’ika Jibrilu zuwa ga Annabi Muhammad (SAW).
Sanadiyyar haka, sai Mala’ika Jibril ya zama mafi alkhairi, kuma mafi falala da matsayi a cikin sauran Mala’iku, saboda falalar saukar da Alqur’anin ta wajen sa shi kadai.
Kuma Allah ya saukar da Alqur’ani mai girma a cikin watan Ramadan, sai watan Ramadan ya zamanto wata mafi girman alkhairi da falala a kan sauran watannin shekara baki daya.
Shiyasa Allah ya shar’anta mana yin azumi a wannan watan saboda falalar saukar da alqur’ani a cikin sa.
 
 ladubban da mutum ya kamata yayi kafin ya fara karanta Alqur’ani:-

1. Ya kasance mutum ya yi Aswaki kafin ya fara karanta Alqur’ani.

2. Mutum ya kasance ya na da tsarki kafin karanta Alqur’ani.

3. Ya kasance an daura alwala kafin fara karanta Alqur’ani.

4. Saka tufafi masu kyau da saka turare mai kamshi kafin fara karanta Alqur’ani.

5. Ya na da kyau mutum ya kalli alkibla yayin da zai karanta Alqur’ani.

6.Yin karatu a fili ko kuma a boye kada ka damu mutane.

7. Daga murya.

8. Daukar Alqur’ni ko kuma yi da ka.

9. Yin karatu da dadin murya, domin kyautata murya (Abu Musal Ash ari ya na karatu annabi ya ji ya ce, karatun al-qur’anin ka na da dadi, kamar murya Annabi Daudu, jiya ina jin ka muryar ka akwai dadi, sai Abu Musal Ash ari ya ce da na san kana nan da na sake daga murya).

10.Banda yin riya.

11.Banda yin sa kamar waka.

12.Akwai yadda a ke yin na kari.

13.Kada ka damu mutane da daddare ko na kusa da kai.

14.Ana so ka fara daga kan gaba.

15.Ka dinga gane ma’anar qur’ani.

16. A dinga tsayawa a kan inda za ka tashi.

17.Ka dinga tsayawa a kan Wakafi da Aya.

18. Ina ya kamata mutum ya tsaya ya kuma tashi.

19.Ya na da kyau idan ka fara karatun alqur’ani ka kammla.


Ba’a son ka dinga karatu da baragada

Similar Apps

مسلم تسبح

مسلم تسبح

0.0

أهلا ومرحبا بكم في هذا التطبيق. تم إنشاء هذا التطبيق من قبل...

Muslim Tasbah Na Hausa

Muslim Tasbah Na Hausa

0.0

Salam barkanku da zuwa wannan application. Dan uwanku ne daga Maiduguri Jahar...

History of 25 prophets

History of 25 prophets

0.0

Barka da warhaka barka da shigowa wannan application Mai albarka...

Tarihin annabawa 25

Tarihin annabawa 25

0.0

Barka da warhaka barka da shigowa wannan application Mai albarka...

قصص الأنبياء

قصص الأنبياء

0.0

Barka da warhaka barka da shigowa wannan application Mai albarka...

بالقرب من المساجد

بالقرب من المساجد

0.0

Barka da warhaka barka da shigowa wannan application Mai albarka...

author
Mashaa-Allahu
Babagana Abatcha
author
Masha Allah Tabarakallah. Very easy during recitation
Baba Ali Shettima